Yan bindiga sun kai hari kan tawagar Shugaba Buhari

‘Yan bindiga sun far wa tawagar Shugaba Buhari kan hanyarta ta zuwa Daura domin share fagen zuwa gida Babbar Sallah da shugaban ya kudirta.

Sanarwar da Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban ya fitar a Talatar nan ta ce, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin da aka kai wa tawagar Buharin a kusa da Dutsinma.inda a ranar Litinin ‘yan bindiga suka kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda.

Tawagar dai ta kunshi ma’aikata da jami’an tsaro gami da ‘yan jaridar da ke aiki a fadar shugaban kasa. An kwantar da mutane biyu a asibiti daga cikinsu a cewar Garba Shehu, sakamakon raunin da suka ji.

More from this stream

Recomended