‘Yan Bindiga Sun Fara Shigar Mata Don Kai Hare-Hare A Wasu Yankunan Sokoto

“Yanzu har shigar burtu suke yi, su yi shigar mata su saka hijabi, su shiga gari su labe. Kullum abin da ke faruwa kenan.” In ji Isa Ambarura.

A Najeriya duk da cewa ana samun saukin hare-haren ta’addanci a wasu yankuna, a wasu yankuna kuma ‘yan bindiga suna shigar burtu ta saka suturar mata suna gudanar da ta’asarsu.

A jihar Sokoto wadda ke arewa maso yammacin kasar har yanzu ana samun koken jama’a a yankin gabashin jihar.

Yankin Illela da shi ma ke gabashin jihar, a cewar jama’ar kusan safiya duk ta Allahs ai ‘yan bindiga sun kai farmaki su kashe ko su sace jama’a.

Bello Isa Ambarura shi ne Wakilin jama’ar yankin a majalisar dokokin jihar Sokoto, ya kuma ce ‘yan bindigan sun sace mutum 7 ciki hadda matar Hakimin kauyen.

Shi ma hakimin kauyen Luggahuru duk a cikin yankin na Illela ya bayyana yadda abin ke haddabar jama’ar sa.

Yankin na Illela wanda nan ne iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar ya kasance sahun gaba inda jami’an tsaro na banga ke taka rawa wajen kare jama’ar su.

Duk da cewa akwai jami’an tsaro na gwamnati a yankin amma a cewar wakilin jama’ar hakan bai hana ‘yan bindihanacin zarafin jama’ar yankin ba.

Har wa yau wasu mazauna yankin sun nuna damuwa akan yanayin da suka tsinci kansu.

“Yanzu har shigar burtu suke yi, su yi shigar mata su saka hijabi, su shiga gari su labe. Kullum abin da ke faruwa kenan.” In ji Isa Ambarura

Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin jami’an tsaro sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a Sokoto bai dauki kiran ba, duk da yake rundunar ta jima tana fadin cewa jami’an na bakin kokarin su tare da neman hadin kan jama’a ga samar da tsaro.

More from this stream

Recomended