
Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun buɗe wuta akan ayarin motocin, Dr.Abiye Sekibo4 darakta janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a jihar Rivers.
Yan bindigar dake sanye da kakakin yan sanda sun buɗe wuta akan ayarin motocin a Rainbow Town dake birnin Fatakwal.
Sekibo yaje ziyarar duba wurin da za a gudanar da taron yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar PDP a jihar.
A yayin kai harin Sekibo na cikin motar sulke kawo yanzu rundunar yan sandan jihar bata fitar da waya sanarwa ba kan faruwar lamarin.