Wasu mutane da da ake zargin yan bangar siyasa ne sun kona ofishin yakin neman zaben, Mohammed Jibrin Barde dantakarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyar PDP.
Ofishin dake kusa da masaukin bakin shugaban kasa dake makotaka da gidan gwamnatin jihar an cinna masa wuta ne da tsakar daren ranar Litinin.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan harin da aka kai kan ofishin amma dai tuni jam’iyar PDP ta dora alhakin kai harin kan jam’iyar APC dake mulkin jihar.
A wata sanarwa da Barde ya fitar ya ce an lalata kayayyaki da dama a harin.