Yadda za ku kare kanku daga masu nuna wariyar launin fata | BBC NEWS

Hujjoji da kimiyya za su iya kawar watsi da nuna wariyar launin fata

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hujjoji da kimiyya za su iya kawar watsi da nuna wariyar launin fata

Kudin goro da kuma ta tsuniyoyin da ake yadawa kan wariyar launin fata sun cika ko ina, amma hakan baya nufin sun inganta. Sai dai masu nuna wariyar a lokuta da yawa ba sa nuna hakan karara.

A wurin wasu mutanen masu kyakkyawar niyya, abin da suka gani da kuma abin da yake a tarihi yana bar wa al’umma wani tunani mara kyau.

Misali: Tunanin da ake yadawa cewa É—aliban da suka fito daga gabashin Asiya sun kware a wajen lissafi, bakaken fata su ma halitta ne, ko kuma a ce Yahudawa sun fi dacewa da kudi. Da yawanmu mun san masu irin wannan tunanin.

Dakta Adam Rutherford wani masanin salsalar ‘yan adam ne kuma mai gabatar da shiri, ya ce, ”Ana matukar nuna wariyar launin fata a fili a wannan zamanin sama da a baya, kuma aikinmu ne mu fadi gaskiya.”

Don haka zai ba mu wasu hujjoji na kimiyya da za su fayyace gaskiya da karya.

Ga wasu hanyoyin biyar da za ka iya rarrabe karya da gaskiya a kimiyyance.

Tatsuniya 1 : Kwayoyin halittar fararen mutane da bakake ba iri daya ba ne

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gaskiya: Dukkan mutane na da kwayoyin halitta iri daya

Asalin nau’in fatar dan adam mai duhu ce. Wadda take bamu kariya daga zafin rana.

Ita ce take karbar zafin ranar da zai iya cutarwa kafin ya lalata sinadarin Folate, daya daga cikin manyan sinadaran Vitamins da jikinmu ke da shi.

Da yawan tsatson da ke samar da gadon ‘ya’ya yana dauke da launin baki. Bambancin halittar da ke cikin tsatson halittar dan adam shi ne ke zama zuwa launin fatar mutane.

Don haka, babban bambancin da ke tsakanin tsarin halittar ‘yan adam na launin fata tsakani farare da bakake daidai ne? Kuskure ne.

Na farko, dukkan ‘yan adam na da kwayoyin halitta iri daya ne – hujjar da ta yi watsi da dukkan abin da muke faÉ—a game da asalin ‘yan Afrika.

Na biyu, Akwai bambancin tsatso na halitta a nahiyar Afrika mai yawa sama da na sauran nahiyoyin duniya in aka haÉ—a duka.

Za a fi samun bambancin kwayoyin halitta kan mutum biyu a Kudancin Afrika, za a fi samun bambanci wajen kwayoyin halittarsu idan aka kwatanta da mutum daga Sri Lanka da Maori da kuma Rasha.

Muna iya banbanta mutane mu ce fari da baki da kuma ruwan kasa amma wadannan launukan da muke gani ba sa nufin bambanci a kwayoyin halittarsu – sai dai ma kamanceceniya – tsakaninsu.

Tatsuniya 2: Babu wani abu mai kama da fifikon halitta

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gaskia: “Fifikon halitta kawai tatsuniya ce”

Muna tunanin wasu yankunan, Æ™asashe ko kuma mutanen da ake killacewa – ko dai a zahiri ko kuma a al’adance – kuma wadannan iyakokin na da mahimmanci wajen shawo kan wadannan matsaloli.

Amma wadannan ba sa cikin abin da tarihi ya bari ko kuma abin da tsatso na halitta shi ma yake bayani akai. Kuma babu wata kasa da ke ta wannan adadi a kasa.

“Mutane sun yi yawon duniya a tarihi, kuma suna jima’i a kowanne lokaci a duk inda suka samu dama,” in ji Dakta Rutherford.

A wasu lokutan wannan wani babban mataki ne a wani dan kankanin lokaci.

Abin da ya fi zama ruwan dare, mutane yawanci na mai da hankali kan kididdiga sama da tsatson dangi – wanda hakan zai iya zama kamar wani asali na yankin ko kuma al’adarsu.

“Kuma duk wani dan Nazi na da alaka da Yahudawa a kakaninsa, in ji Dakta Rutherford, “Duk wani farar fata na da kakanni a Gabas Ta Tsakiya. Duk mai nuna wariyar launin fata na da alaka da Afrika ko Indiya ko gabashin Asiya.”

Tatsuniya 3: Jamus ta Jamusawa ce, Turkiyya ta Turkawa ce da dai sauran bambance-bambance

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wane ne na farko a ko wacce kasa?

Wasu mutanen sun fuskanci damuwa kan ‘yan gudun hijirar da ‘yan ci rani da ke shiga kasarsu, wannan wani al’amari ne da kusan ake fuskanta a wurare da yawa a fadin duniya.

Cikin misalan bayan nan, wani harbin bindigar kan mai uwa da wabi da aka yi a wajen wani shan tabar shisha a Hanau, Jamus, wata hujja ce da masu fafutuka kan kora ko kuma kashe ‘yan ci rani.

Wadanda ke da rajin korar ‘yan ci rani sun ta nuna bacin rai ta hanyar yada kalamai irinsu: Jamus ta Jamusawa ce, Faransa ta Faransawa ce, Turkiyya ta Turkawa ce, Italiya ta Italayiwa ce, an yi ta amfani da su don nuna kin jinin ‘yan ci rani.

“Ku koma in da kuka fito” wani kalamin wariya da ya game duniya.

Tatsuniya ta 4: Gwajin kwayoyin halitta kan tabbatar da cewa mutum fari ne 100 bisa 100

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana iya gadar kwayoyin halitta daga kakannin mutum kuma zai iya gada daga kakan shi na 11

Masana ilimin salsala da kakanin suna ba mu mamaki – sai kuma masu nuna wariya a takaice.

Shafukan intanet irin su Stormfront masu rajin kare fararen mutane ne ke kula da su, suna amfani da kwayoyin gwajin dan adam da suke samu daga kakaninsu a matsayin shaida cewa su jinin Yahudawa ne 100 bisa 100.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ba a gadan kwayoyin halitta duka kaf daga kakanni

Kwayoyin halitta na da matukar amfani wajen bibiyar tarihin zuri’a – kuma suna taimakawa wajen gano wani dan uwa da ya bata ko kuma mahaifi.

5. Bakaken mutane sun fi juriyar gudu sama da farare

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Yadda Usain Bolt ke samun nasarar fintinkau na daya daga cikin abin da ya kara hassala wannan tunani

Mutum na karshe da ya yi takarar mita 100 a wasan karshe a gasar Olympics ya yi ta ne a 1980.

Tun daga nan, bakake ne suka mamaye wannan gudun. Wannan ya kara rura wutar tunanin cewa bakaken Afrika suna cinye wannan gasar ne saboda tsatson kwayoyin halittar da suka gada daga kakanninsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani bakar fata dan Amurka na gudu

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...