
Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE
Mutumin da ya yi kisan ya tsere har yanzu ba mu kai ga gano inda yake ba, ba kuma mu samu wani makusancinsa ba
Rudunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai shekara 45 a karamar hukumar Kaugama ta jihar.
Cikin wata hira da BBC, kakakin rundunar SP Audu Jinjiri ya ce sunan mutumin da aka kashe Sale Dange, kuma an kashe shi ne ta hanyar caka masa wuka.
Ya ce a ranar Litinin ne wani mutum da ake zargin shi ya yi kisan mai sunan Umar Jalo mazaunin garin Dakaiyyawa, ya iske marigayin Sale Dange tare da matar da ya saka cikin ƙasa da mako guda.
Abin ka da mai zafin kishi bai tambayi wanene wanda take tsaye da shi ba ko kuma alaƙarsu, kawai sai ya fidda wuƙa ya burma wa marigayin, wanda kafin a ƙarasa asibiti ya ce ga garinku nan.
SP Audu Jinjiri ya ce: “Da misalin karfe 2:30 na rana ne wani mutum da ake kira Umaru wanda ba a san daga inda yake ba ya zo wannan Ƙaramar Hukuma ta Kaugama inda ya samu wani Sale Dange É—an shekara 45 na Æ™auyen DaÆ™ayyawa da ke Æ™aramar hukumar Kaugama.
“Ya tsinkaye shi ne tare da matarsa a tsaye da ya sake ta kwana uku da suka wuce kawai sai yazo ya daÉ“a masa wuÆ™a take ya faÉ—i magashiyyan muna samun rahoto muka nufi asibiti kan kace komai ya mutu.”
Binciken ‘yan sanda ya tabbatar da cewa Umar Jalo, ya saki matarsa ne saki uku, wanda a koyarwar addinin musulunci ta haramta a gare shi a wannan lokacin, kamar yadda SP jinjiri ya bayyana.
Rundunar ‘yan sandan ta ce, a bayanan da ta samu daga matar da aka yi kisan dan ita, sun nuna Umar Jalo É—an asalin jihar Bauchi ne a garin Azare, abin da ya sanya su bibiyar Jalo har Bauchi.
Sai dai rundunar ta gaza samun wannan mutum da ya tsere ko kuma wani É—an uwansa ko makusancinsa.
“Da zarar kuma an kama shi za mu gurfanar da shi gaban kotu domin girbe abin da ya aikata,” in ji SP Jinjiri.
A gefe É—aya shi ma mamacin an gaza samun ‘yan uwansa, wannan dalili ya sanya aka ajiye shi a É—akin ajiye gawarwaki kafin samun makusantansa.