Yadda sojojin Chadi ‘suka kashe ‘yan Boko Haram’ 1,000

an kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

An kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu

Rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 1,000 a wani samame da ta kai yankin Tafkin Chadi.

Kakakin rundunar sojin Kanar Azem Agouna ya ce an kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu.

Shugaba Idriss Déby ya ziyarci yankin Tafkin na Chadi. Ya ce babu dan kungiyar Boko Haram ko daya da ya rage a yankin.

Ya yi takaici kan yadda ya ce an bar Chadi ita kadai take fatattakar mayakan na Boko Haram a fadin Tafkin na Chadi, wanda ke da iyaka da kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

An kaddamar da farmakin ne bayan da a watan jiya sun kashe dakarun Chadi kusan 100 a harin da suka kai musu a yankin.

Har yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sojojin Chadin kuma Boko Haram bata ce komai ba.

Hakkin mallakar hoto
BOKO HARAM VIDEO

Image caption

Mayakan Boko Haram suna da mafaka a yankin Tafkin Chadi

More from this stream

Recomended