Yadda rikicin kabilanci ya janyo takaddama a Taraba | BBC Hausa

Wasu al’ummomin Hausawa da Fulani da kuma barebari ‘yan asalin garin Wukari da ke jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya sun zargi hukumomi da hana su komawa mazauninsu tun bayan rikicin da aka yi mai nasaba da kabilanci da kuma addini shekara 7 da ta gabata, abin da ya tilasta masu zaman gudun hijira a wasu yankunan jihar.

Mutanen na unguwar Sabon Gari, sun ce kimanin shekara 5 ke nan da ta gabata suke kokarin komawa gidajensu amma abin ya ci tura.

Rikicin na shekara ta 2013 dai ya yi sanadiyyar rasa dimbin rayuka da dukiyoyi a garin na Wukari. Jihar Taraba dai na daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikce tsakanin kabilu, musamman Jikunawa da Tibabe da kuma kabilun da ke da nasaba da Hausawa.

Abdu Ali, daya daga cikin mazauna yankin na Sabon gari ya ce suna gudun hijra a wasu wuraren kuma bayan shekarun da suka yi ba a gidajensu bane suka fara kokarin komawa mazauninsu.

Ya ce “wasu daga cikinmu har sun yunkura ma sun fara kai kayan aiki suna fara gini toh sai a turo (matasa) sai su zo su rusa mana wadannan gidaje da muke ginawa. Suyn riga sun kona wurin ya koma fili,”

“Muna zargin Sarkin Wukari da (shugaban) karamar hukumar ta Wukari su suke tura su suke rushe mana gidaje. Mun yi iya bakin kokarinmu mun (zabi) wasu mutane daga cikinmu aka tura sai aka ce ai Sarkin yana fushi da wasu mutane mazauna sabon garin Wukari.” in ji Abdu Ali.

Amma Danladi Baushe, wanda shi ne Madakin Uka Wukari ya karyata zargin al’ummar na Sabon Garin inda ya ce “mun sanar da kowa cewa duk wanda zai zo ya tabbatar ya zauna dai-dai wurinsa kada ya yadda ya shiga gidan wani ko taku daya gidan makocinsa,”

Game da zargin da al’ummar suka yi na cewa Sarkin na Wukari ya ki amincewa mutanen su dawo gidajensu ba, Baushe ya ce “karya ne ana so a bata masa suna ne.”

Ya kuma ce akwai wadanda suka dawo amma wasu na kokarin dawowa kafin karshen shekarar nan.

More from this stream

Recomended