Yadda Rikicin Boko Haram Ya Shafi Harkokin Kasuwanci

A Najeriya, sama da shekaru goma kenan, da dakarun kasar suke ta fafatawa da mayakan kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya, musamman a arewa maso gabashin kasar.

Jihar dai da ta fi fuskantar hare-haren kungiyar, ita ce ta Borno, lamarin da ya yi mummunan tasiri akan tattalin arzikin yankin.

Wannan tasiri na koma-baya da aka gani musamman a ‘yan shekarun da suka gabata, ya jefa al’umar yankin musamman ‘yan kasuwa cikin halin ni-‘yasu.

Bincike ya nuna cewa, fannini da dama na harkokin kasuwanci a jihar ta Borno, sun fuskani koma baya matuka.

Koda yake, ba a kare a wuri guda ba, domin yayin da wasu bangarorin kasuwanci suka farfado, wasu kuwa har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba.

Gwoza, ita ce karamar hukumar farko da ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram suka taba kwacewa, an kuma taba rufe babbar kasuwa garin, sanadiyyar hare-haren kungiyar, ko da yake, al’amura sun daidaita domin tuntuni aka bude kasuwar

“A gaskiya lokacin da aka rufe kasuwar nan mutane sun shiga damuwa, a lokacin da jarrabawa na Boko Haram ya same mu, an rufe kasuwar nan saboda kada su samu dama su zo su abkawa mutane.” Inji tsohon shugaban karamar hukumar ta Gwoza, Alhaji Abdullahi.

Ya kara da cewa, “amma da ikon Allah da sojoji suka tsaya tukuru, mutanenmu sun koma gida, kasuwan nan bude ta, a Gaskiya yanzu kasuwr tana cika makil.”

Sai dai ba kamar ‘yan kasuwar ta Gwoza ba, fannin sarrafa burodi ya shafu matuka, kuma har yanzu a cewar shugabansu, Malam Bukar Mustapha, harkar gasa burodi, ba ta dawo yadda take ba.

“Kafin zuwan wannan matsalar tsaro, muna da gidajen burodi da suka kai 500… amma yanzu ba su fi 150 ba.” Inji Mustapha.

Ya kara da cewa, hare-haren da aka kai a yankunan “Bama, Gamboru Ngala, Gwoza, Damboa, Monguno da Damasak,” har yanzu babu wanda ya samu karfin tasowa.

More News

Rundunar Sojan Najeriya Ta Fitar Da Sunayen Sojojin Da Aka Kashe A Jihar Delta

Rundunar sojan Najeriya ta fitar da hoto da kuma sunayen sojoji 16 da aka yiwa kisan gilla a jihar Delta. Ranar Alhamis ne aka kashe...

Wasu ƴan mata a Najeriya sun ƙirƙiro janareta mai amfani da fitsarin mutum

Wasu matasa ‘yan Najeriya hudu sun kirkiro wani janareta mai amfani da litar fitsari don samar da wutar lantarki ta sa’o’i shida. Ƴan matan –...