Yadda PDP, ZLP Suka Kalubalanci Gwamna Akeredolu Na APC a Zaben Ondo

Zaben na ranar Asabar na zuwa ne kasa da wata guda bayan wanda aka yi a jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriyar, wanda PDP ta lashe.

A wannan zabe mai ‘yan takara 17, gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, na neman wa’adi na biyu yayin da manyan ‘yan adawa EyitayoJegede na Jam’iyyar PDP da kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP ke kalubalantarsa.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal da ya yi hira da wasu mazauna birnin Akure da wasu sassan jihar ta wayar tarho, ya ruwaito cewa, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ko da yake, wasu kafofin yada labaran kasar sun ce an dan samu ‘yar hatsaniya a karamar hukumar Akure ta Kudu, lamarin da har ya kai ga harba bindiga, amma hukumomin tsaro sun ce babu wanda ya ji rauni.

Sannan akwai rahotanni da ke nuna cewa wasu jam’iyyu na zargin an tafka magudi a zaben.

Hakan na nufin ba kamar yadda aka saba ganin yadda manyan jam’iyyun kasar biyu suke mamaye zabuka ba, a zaben jihar ta Ondo manyan jam’iyyu uku ne suke gwada kaiminsu.

A zaben 2016, gwamna Akeredolu na APC da Mr. Ajayi na jam’iyyar Zenith Labour Party, (ZLP) wanda shi ne mataimakin gwamna Akeredolu, sun ka da Mr Jegede na jam’iyyar PDP.

Amma Ajayi, ya raba gari da gwamna Akeredolu inda ya sauya sheka ya koma ZLP a wannan zabe don kalubalantar tsohon maigidansa.

Rahotanni sun ce tun da misalin karfe 8:30 na safe aka bude rumfunan zabe da dama a sassan jihar ta Ondo mai kananan hukumomi 18.

A kuma lokacin hada wannan rahoto, an rufe da yawa daga cikin rumfunan zaben.

Wannan shi ne karo na biyu da manyan jam’iyyun kasar biyu, wato APC da PDP suke gwada farin jininsu a zaben jihohi wanda wasu masu fashin baki ke cewa zai iya zama manuniya ga abin da zai faru a zaben 2023.

A ranar 19 ga watan Satumba, gwamna mai ci Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihar ta Edo bayan da ya kada abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na APC.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...