
Asalin hoton, Twitter/@CAS_AMSadique
Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da sakamakon binciken farko da ta gudanar game da mutuwar matuƙiyar jirgin saman yaƙi Tolulope Arotile.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce binciken da suka gudanar da farko ya nuna cewa marigayiyar ta mutu ne sakamakon buguwa a kanta bayan da wasu da suka yi makarantar sakandare tare suka bugi motar da take ciki.
Rundunar ta yi wannan bayani ne sakamakon yadda mutane ke ci gaba da neman ƙarin bayani game da mutuwar Arotile.
Mutuwar Arotile ranar 16 ga watan Yulin 2020 a sansanin rundunar sojin saman da ke Kaduna ya tashi hankalin al’ummar ƙasar.
Abin da ya faru
Sanarwar da kakakin rundunar sojan saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar Ranar Lahadi, ta ce abin da ya faru shi ne ranar goma sha hudu 14 ga watan Yuli, matuƙiyar jirgin yaƙin Tolulope Arotile da ƙarfe 10 na safe ta karbi wani kira daga abokin aikinta Flying Officer Perry Karimo inda ya bukaci ta zo sansanin sojin sama na Kaduna don su tattauna yadda za su koma aiki Enugu.
A cewar sanarwar ‘yar uwar marigayiyar ce mai suna Mrs Adegboye ta ɗauko ta a mota zuwa sansanin sojan don amsa kiran da aka yi mata.
Bayan Flying Officer Arotile ta isa sansanin ne sai ta saka wayarta caji a gidan wani Squadron Leader Alfa Ekele sannan ta wuce zuwa kasuwar bariki ta mammy market don a gurza mata kwafin wasu takardu.
Asalin hoton, Twitter/@CAS_AMSadique
Bayan ta kammala za ta koma ne da ƙarfe 4:30 na yamma, sai wasu waɗanda suka yi makarantar sakandire tare su uku suka wuce ta cikin mota.
“Da suka hange ta sai suka koma da baya da sauri don su yi mata magana, lamarin da yasa suka banke ta da mota ta baya, inda kanta ya bugu da gefen hanya sannan suka bi ta kanta” a cewar sanarwar.
Sanarwar tace nan take aka garzaya da Flying Officer Arotile zuwa asibitin sojojin sama na Kaduna, to sai dai ɗaya daga cikin waɗanda suke cikin motar wanda ma’aikacin jinya ne ya fara da bada agajin gaggawa.
Rundunar ta tabbatar da cewa Flying Officer Arotile ta mutu ne sakamon buguwa da kanta ya yi a gefen titi da kuma jinin da ya zuba daga jikinta mai yawa.
Halin da ake ci ciki
An kama wadanda ake zargi da buge marigayiyar da mota, inda aka gudanar da bincike kuma an tabbatar da cewa direban bai sha giya ko wani abu mai gusar da hankali ba sai dai an gano direban bashi da lisisin tuki a cewar sanarwar da rundunar sojin saman ta fitar.
Kasancewar lamarin ba laifi ne na ganganci ba za a mika lamarin ga ‘yan sanda da nufin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu.
Haka kuma sanarwa ta ce jami’an ‘yan sandan caji ofis na Kawo da kuma rundanar ‘yan sandan jihar Kaduna da jami’an hukumar kare afkuwar hadura dukkansu sun taimaka yayin gudanar da binciken.
Tun bayan mutuwar Arotile ne dai wasu ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta suka rika nuna shakku game da abubuwan da suka yi sanadiyyar mutuwar Arotile.
Marigayiyar wadda ‘ƴar asalin jihar Kogi ce, an bayyana cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaƙi da ‘ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.