Wani bincike da aka assasa shi domin gano yadda kudin-cizo ke yaduwa ya nuna cewa kudin-cizon ya riga dan’adam fara rayuwa a doron kasa.
Kuma binciken ya nuna cewa kwarin sun gabaci zuwan abokan rayuwarsu (Jemagu) doron kasa, da fiye da shekara miliyan 50.
Shi dai kudin-cizo yana iya shan jinin da ya rubanya nauyin jikinsa sau uku a lokaci guda.
Yana kuma iya rayuwa na tsawon shekara guda bayan cikar girmansa – abinda kwari da dama ba su iyawa.
Akwai nau’uka na kudin-cizo da suka kai 100, yawancinsu suna rayuwa ne a jikin Jemagu, nau’i biyu ne kawai suke rayuwa a tare da dan’adam.
Mujallar Current Biology ita ce ta wallafa wannan sakamakon binciken mai cike da abin mamaki.
Binciken ya kuma gano cewa kudin-cizo wani irin halitta ne da ya sha daban, inda dabi’unsa da dama suka banbanta da na sauran kwari.
Yawancin na’ukan kudin-cizon da masu binciken suka yi nazari a kansu suna rayuwa ne a jikin Jemagu wadanda ke cikin koguna.
Kuma suna rayuwa ne ta hanyar shan jinin Jemagun.
Bayan da masu nazarin suka dauki sinadaran kwayoyin halittar nau’ukan kudin-cizon ne suka samu damar yin bincike kan tsatso, da asalin rayuwarsu.
Dr Steffen Roth, na University Meseum Bergen, da ke kasar Norway, wanda shi ne ya jagoranci nazarin, ya ce abin mamaki na farko da suka gano shi ne kudin-cizo ya riga Jemage fara rayuwa a duniya.
Alhali kuwa a baya an yi zaton cewa kudin-cizo sun fara rayuwa ne a jikin jemagu.
Sai dai ya ce ba a san ko wadanne halittu ne kudin-cizon suka rinka rayuwa tare da su ba a wancan lokacin.