Yadda kisan wasu jami’an Laberiya ya sa kasar neman daukin Amurka

Shugaba Weah

Shugaban kasar Laberiya George Weah, ya roki Amurka da ta taimaka wajen binciken musabbabin mutuwar wasu manyan jami’ai uku dake aiki da ma’aikatar kudin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Laberiya wato LINA ya rawaito.

Lamarin ya janyo jita-jitar cewa kisan na su nada alaka da siyasa.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito shugaba Weah na kira ga mutane da kada su yi zato, kuma su jira sakamakon bincike.

Mista Weah, ya umarci ministan shari’a Frank Musa Dean, da ya hada guiwa da sauran jami’an gwamnati da kuma na gwamnatin Amurka, domin tabbatar da an gudanar da zuzzurfan bincike.

An bayyana sunan daya daga cikin wadanda aka kashe da Emmanuel Nyeswua, wanda kuma shine shugaban hukumar binciken kudi ta cikin gida ta kasar.

Sauran biyun suna aiki da Hukumar Haraji ta Liberia, amma hukumomi basu ambaci sunansu ba.

Akwai kuma wasu karin mutanen da aka kashe da suka hadar da Ista Nyeswa, wanda aka tsinci gawarsa a gidansa a Monrovia, babban birnin kasar, ranar Asabar.

Da wani jami’i a hukumar tara kudaden shiga ta Laberiya wanda ya mutu a hatsarin mota a Monrovia a ranar 4 ga Oktoba.

Akwai kuma karin wasu jami’ai biyu a hukumar tara harajin wadanda aka tsinci gawar su a cikin wata mota.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato shugaba Weah na cewa an nemi ofishin jakadancin Amurka da ke Monrovia da ya taimaka, ciki har da neman likitan da zai binciki gawarwakin don sanin abin da ya yi sanadin mutuwarsu.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...