Yadda ake yaudarar ‘yan kasar Bangladesh zuwa yin bauta a Libya

Dan Bangladeshi ya na kallon tekun da ke tashar ruwan Palermo da ke Italiya

Asalin hoton, Kate Stanworth

A cikin jerin wasikun ‘yan jaridar Afirka da muke kawo muku, dan jarida Ismail Einashe ya hadu da wani mutum da ya tuna bakar wuyar da ya sha a hannun mutumin da ya yaudari iyayensa kan sama masa aiki a Libya, da yadda ya kubuta.

Matashin dan ci rani dan asalin Bangladeshi, da ke birnin Palermo mai tashar ruwa a kasar Italiya, yana zaune a kan kujera cikin damuwa, yana wasa da wayar salular da ke hannunsa a lokacin da yake tuna halin da ya samu kansa a ciki a lokacin da yake kasar Libya.

A watan Disambar 2019, lokacin yana dan shekara 19, Ali wanda ba sunan shi na asali ba ne, shi da iyayensa suka yanke shawarar ya yi tafiyar kasada domin neman aikin yi.

An kammala komai bayan ya hadu da Ejan din da zai shirya masa tafiyar. A zahiri masu safarar mutane ne, wadanda suke gudanar da kasuwancin a boye, da yaudarar matasan Bangalai ta hanyar alkawari da karairayi da kwadaita musu arziki.

Wani dan Bangladeshi da a yanzu yake Sicily, ya bayyana yadda ya bar gida a shekarar 2016, lokacin yana dan shekara 16, duk dai karkashin shirin Dalal wato Eja.

“Iyayena na son na yi kaura tun ina dan karami amma hakan ba ta samu ba, sai suka yanke shawarar biyan Eja kudi domin su yi min fasfon boge,” a ciki aka rubuta shekararsa 21.

Ejan ya yi kokarin zama abokin Ali, inda ya dinga ba shi kwarin gwiwar tafiya kasar Libya, ya ma taba gayyatar shi cin abincin dare a gidansa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Yawancin iyaye sun amince safarar ‘ya’yansu zuwa kasar Libya zai kawo sauyin rayuwa a gare su

Matashin na aiki ne a kantin sayar da kayan kwalliyar mata a wajen babban birnin Bangladesh, Dhaka, shekara da shekaru shi kadai ke taimakon iyayensa wadanda suke zaune kauyen Padma da ke wajen birnin.

Masu safarar mutanen sun fi maida hankali kan matasa irinsu Ali, wadanda ke kokarin tserewa talauci da fatan samun ingantacciyar rayuwa.

Sai dai, kalilan daga cikinsu da suka je kasar Libya ne suka kai labari, sakamakon yadda yaki ya daidaita kasar da tsananin wuya da azabar da masu safarar mutanen ke janyo musu fadawa ciki har da tsananin bauta, duk da sunan neman ingantacciyar rayuwa.

“Ban san komai game da Libya ba,” in ji Ali.

Daga baya mai safarar mutanen ya gana da iyayen Ali, ya shaida musu É—ansu zai iya samun har sama da dala 500 a kowanne wata amatsayin ma’aikacin kamfani a kasar Libya.

Iyayen Ali sun shaida ma sa ba su da kudin da za su biya ma sa domin yn tafiyar, amma haka mutumin ya dinga ba su kwarin gwiwa bayan ya gano su na da kadarori, sai ya ba su shawarar saida wasu daga ciki wato Shanunsu domin biyan kudin balaguron Ali.

An tsare shi domin kudin fansa

Ali ya dauki mako guda kafin isa Libya -tafiyar mota suka yi daga birnin Dhaka har zuwa Kolkata na indiya, daga nan kuma sai jirgi daga Mumbai zuwa Hadaddiyar daular larabawa zuwa birnin Alkhahira na kasar Masar.

Amma lokacin da suka sauka a filin jirgin Bengazi, sai ya samu kan shi a birni mai cike da hayaniya da harkalla, babu jami’an tsaro ko ‘yan sanda.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Yawancin gine-ginen birnin Benghaz sun ruguje, wadanda yakin shekara goma da kasar ta fuskanta ya lalata

Yana isa aka kama Ejan din tare da tasa keyarsa zuwa gidan kaso, tare da karbe duk kudin da suke tare da shi, suka kuma rike shi domin kudin fansa.

Sai da iyayensa suka saida shanu biyu, kafin suka samu kudin kubutar da shi.

Dakin kurkukunsa dan karami ne dauke da wasu yamulallun katifu, su 15 ne a ciki duka ‘yan Bangladesh.

Wadanda suka gagara biyan kudin fansa ko abinci ba a ba su, ga bakar wuyar da ake gana musu.

“A kan ido na aka lakadawa wani duka, jini na zuba daga kan shi. Ba su kai shi asibiti ba,” in ji Ali.

A shekarun da suka gabata, sha’anin tsaro ya tabarbare a Libya, musamman ga Bangalai mazauna da masu safarar mutane ke tsare da su.

A watan Mayun 2020, an kashe ‘yan cirani 30, 26 daga ciki ‘yan Bangladesh ne, an harbe su a gidan ajiye kaya da ke Mizdah a kusa da babban birnin kasar Tripoli.

Wani da ya kubuta ya ce ‘yan uwansu sun gagara biyan kudin fansa.

Bayan an sako Ali, ya bige da aiki a gidan ruwan robar daya daga cikin masu safarar mutanen, har na watanni uku a Benghazi, kafin ya koma aiki kamfanin yin tayal.

Kamar kusan Bangalai 20,000 da a halin yanzu akai kiyasin su na kasar Libya, Ali ya fi su shan wuya, saboda aiki babu albashi, ga bakar wuyar da ya ke sha a inda ya ke zaune.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
‘Yan ciranin Bangladesh kamar Ali, wanda baya cikin hoton nan, na daga cikin ‘yan kasashe uku da ke sahun gaba cikin masu tafiyar kasadar ketara tekun Mediterranean daga Libya

“Idan muka dakata daga yin aiki ana lakada ma na duka, a hantare mu ko a yi wurgi damu. Ba a biyan mu albashin aikin da muke yi, wata rana daya daga cikinmu ya fasa bulo daya bisa kuskure, kawai wani ya zo ya dinga dukan shi, in ji Ali.

Matashin yana zaune a gidan mai kamfanin bulon, kuma a rufe cikin wani daki.

“Shi ya ke daukar mu ya kai wurin aiki, idan mun gama aiki ya dawo da mu ya sake rufewa. Akwai masu gadi biyu da ke sanya mana ido. Ba a biyan mu albashi, babu abinci, don haka muke son tserewa.

“Daya daga cikinmu ya yi kokarin guduwa, amma ya fado daga hawa na biyu ya karya kafa.”

Bayan kokarin tserewa a lokuta daban-daban babu nasara, wani dan Libyan mai kirki ya taimakawa Ali inda yake fakewa a masallaci.

Sai ya ke ganin hanyar karshe da ta rage ma sa ita ce ya sake tuntubar masu safarar mutane, a wannan karon ya ketara tekun Mediterranean zuwa kasar Italiya.

Manyan kifaye a teku

Iyayensa sun sake biyan kudi – ya yi kiyasin kudin da aka kashe daga balaguron Bangladesh zuwa Italiya sun kai dala 4,000, lamarin da ya janyo wa iyayensa tarin bashi.

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto,
Kwale-kwalen ‘yan cirani da aka yasar a kudancin Sicily

Ketarawar ta watan Yulin bara, ta zama daya daga cikin munana da suka faru a tarihin tafiyar kasadar ‘yan cirani da ta firgita Ali, da sauran ‘yan cirani 79 da ke cikin kwale-kwalen.

“Kwanaki biyu babu abin da muke gani sai teku, babu tsandauri. Sai muka ga manyan kifayen shark guda biyu daga can nesa, wasu na fadin shi kenan za su zo su cinye mu. Na yi tunanin shi kenan, ta mu ta kare!'”

Daga bisani an kubutar da su, inda aka kai su tsuburin Lampedusa kafin a kai su Sicily.

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto,
Dubban ‘yan Bangladesh da ke zaune a Sicily, yawanci su na aikin jiran kantina

A yanzu Ali yana zaune a wani katon sansanin ‘yan cirani da ke wajen Palermo, da ke Sicily, tare da sauram matasan ‘yan cirani daga kasashe kamar Najeriya, da Gambia da Senegal.

A Libya babu wata hanyar da ‘yan Bangladesh da sauran kasashe ke samun damar magana da juna, mau safarar mutanen na shiya kurkuku daban-daban da ake ajiye ‘yan kasashe guda a kowanne.

Aiki a wurin saida Sushi

Ali ya yi aikin wucin a Italiya, sai dai anki amincewa da bukatar da ya shigar ta samun kariya, amma ya sake shigar da wata takardar kan hakan.

Ya koyi hada ayyuka guda biyu, a yanzu ya na aiki a Palermo a gidan saida abincin Sushi, da wasu ‘yan ciranin Afirka.

Asalin hoton, Kate Stanworth

Bayanan hoto,
Ali ya ce ba kamar a kasar Libya ba, a Italiya ‘yan Bangaladesh da Italiya na na mu’amala tare

Kamar wadanda suka zo daga baya-bayan nan, ana biyan sa abin da bai taka kara ya karya ba a aikin da ya ke yi, wanda ‘yan asalin Sicily ba za su taba amincewa da shi ba.

Ana biyansa dala 570 a kowanne wata amma ya na aikin kwanaki shiga a kowanne mako babu takamaimai lokacin tashi, amma idan ‘yan kasa ne suka aikin kwanaki biyar a mako da albashin 870.

Shekarun da suka gabata ‘yan Palermo na matukar kaunar Sushi, sai dai ‘yan Japan kalilan ne ke zaune a birnin, sai gidajen sayar da abincin Æ´an China suka shiga harkar, suka fara sayar da nau’in abincin ciki har da su kaguwa da kyat da sauransu.

Ali, bai taba sanin Sushi ba sai da ya je birnin, a hankali ya fara jin dadin nau’in bincin, mai dauke da danyen naman kifi.

“Ina son koyon yadda ake hada shi baki daya, na kuma koyi nau’in abincin ‘yan italiya,” in ji Ali.

(BBCHAUSA)

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...