HomeHausaYadda aka yanke wa masu satar mutane hukuncin ɗaurin rai da rai...

Yadda aka yanke wa masu satar mutane hukuncin ɗaurin rai da rai a Sokoto

Published on

spot_img
Police

Asalin hoton, Getty Images

Ƴan uwa da masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane huɗu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kotun dai ta yanke musu wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin garkuwa da wani fitaccen ɗan kasuwa a shekarar 2013, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa saboda jigata da ɗimautar da ya yi.

Ba kasafai ake jin kotuna na yanke wa masu satar mutane hukunci irin wannan hukunci ba, musamman a yankin arewacin ƙasar, inda hare-haren ƴan fashin ke ƙara ta’azzara.

Duk da tsawon shekarun da aka kwashe bayan sacewa tare da yin garkuwa da marigayi Alhaji Abubakar Dankure, makusantan ɗan kasuwar sun ce ɗaurin rai-da-rai da kotu ta yanke wa masu garkuwar ya rage musu zafi da raɗaɗin aika-aikar da aka tafka musu.

Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin Alhaji Aminu Abubakar Dankure ya ce, ko da yake hukuncin ba zai iya cike giɓin da mutuwar mahaifinsu ta bari ba, amma dai sun samu ƙwarin gwiwar cewa an kamanta adalci.

“Hukunci dai kamar yadda aka yi shi, mun gode Allah. Kuma babu wani abu da bai yi mana daidai ba cikin hukuncin.”

Sai dai ya ce duk da cewa sun ji daɗin hukuncin hakan ba zai goge tabon rashin uba da suka yi ba, “sai da i hakan ya fi da a ce haka aka ƙyale su.”

Masu garkuwa sun sace mahaifinsu Alhaji Abubakar Dankure inda ya shafe kwana shida a hannunsu.

Daga bisani bayan biyan kudin fansa ne suka sake shi, sai dai kuma sakamakon jigata da ya yi sai Allah ya yi masa rasuwa bayan ‘yan kwanaki.

Jami’an tsaro sun yi nasarar kama masu laifin su shida, ko da yake biyu sun rasu, inda aka gurfanar da su a gaban Kotun Tarayya a 2013.

Bayan saɓata-juyata irin-na shari’a kusan tsawon shekara takwas a makon jiya, Mai Sharia Lurwanu Aikawa na Babbar Kotun Tarayya da ke Sokoto ya yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai.

Barista Labaran Sha’aibu Magaji lauyan masu ƙara, ya ce: “Ya kamata a sanar da masu sauraro cewa akwai mutum biyu daga cikinsu da suka mutu yayin da ake tsare da su saboda dalili na rashin lafiya.

“Yanzu saura su hudu kenan da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai.

Bayan hukuncin ɗaurin, kotu kuma ta bayar da umarni su mayar da kuɗaɗen da suka karɓa na fansa har dala dubu 300.

“Na biyu kotu ta yanke hukuncin cewa su bai wa iyalan marigayin kuɗi naira miliyan 50 don rage musu damuwa na halin da suka fuskanta yayin da aka sace mahaifin nasu.

“Kana an sake umartarsu da ba da naira dubu ɗari-ɗari ga Alhaji Aminu Dankure da Nasiru, da zai zamanto a madadin kudin jirgi da suka biya na zuwa Abuja don biyan kuɗin fansar baban nasu a Kwali,” a cewar lauyan.

Masu rajin kare hakkin dan adam ma, sun tofa albarkacin su game da wannan hukunci. Barista Muhammad Mansur Aliyu na daga cikinsu, kuma ya ce hukuncin abu ne mai daɗi.

“Hukuncin ya yi wa al’umma da kuma mu kanmu lauyoyi daɗi saboda ya tura saƙo na musamman ga dukkan wanda yake wannan aiki na satar al’umma.

“Saboda an yanke musu hukuncin cewa lallai za su zauna gidan yari har ƙarshen rayuwarsu. Ka ga kuwa ai lallai kowa zai ji daɗin haka.”

Mutum hudun da aka yanke wa hukuncin dai, suna da damar daukaka kara nan da kwana 90.

Lamarin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa na ci gaba da ta’azzara a Najeriya.

Hakan ce ta a watan Yulin bara Majalisar Dattawan kasar ta amince da hukuncin daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.

A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ne ga mutanen da aka kama da laifin.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...