Yadda aka tarwatsa masu zanga-zanga a Kano

BBC

A ranar Asabar ne wasu matasa maza da mata suka shirya wata zanga zanga domin nuna rashin goyon baya kan kirkiro wasu sabbin masarautu a Kano, karkshin kungiyar ”Kano First.”

Masu zanga-zangar sun shirya taruwa ne a harabar Kofar Kwaru da ke gidan sarkin na Kano, daga nan sai su yi tattaki zuwa harabar gidan gwamnatin jihar don nuna rashin goyan bayansu ga yunkurin na gwamnatin.

Toh amma hakan bai yi wu ba sakamakon wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka mamaye gurin tun da sanyin safiya dauke da manyan hotunan Sabon Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero da na Marigayi Sarki Ado Bayero.

Sakamakon haka ne ya tilasta wa masu zanga-zangar koma wa bakin kotun Kofar Kudu da ke kallon gidan sarkin Kano domin gudanar da taron na su wanda shi ma daga baya aka tarwatsa su.

Nura Ma’aji na daya daga cikin jagororin kungiyar Kano First ya kuma shaida wa BBC cewar:

“Mun fito ne don mu nuna rashin goyon bayanmu kan kirkiro wasu sabbin masarautu a Kano, don ba shi mutanen Kano ke bukata ba, akwai matsalolin da ke damun al’ummar jihar Kano musamman samar da ingantattun kayan more rayuwa, kuma bisa ga fahimtarmu, an tasar wa rusa tarihinmu na masarautun Kano”.

Ya kuma bayyana cewa “ba a nemi ra’ayin mutane ba kawai a ce cikin abin da bai wuce kwana uku ba a ce a gabatar da doka, an yi karatu na biyu, an kuma amince da ita kuma an sa mata hannu, da alama dai akwai lauje cikin nadi wajen gaggawar amincewa da hakan.”

A wani bincike da BBC ta gudanar, ta gano cewa akwai motoci masu dimbin yawa dauke da hotunan gwamnan Kano da kuma mataimakinsa a inda aka ajiye su a wajen Kofar Kwaru ta gidan sarki da tsallaken filin gidan Marigayi Mallam Nasir Kabara, zuwa kofar gidan Kogunan Kano da ke unguwar Jar kasa.

Gwamnatin jihar ta tsayar da ranar Asabar a matsayin ranar da za a mika takardar kama aiki ga sabbin sarakunan da aka kirkiro a jihar ta Kano, duk da cewar wata babbbar kotun jihar a ranar Juma’a ta bayar da umarnin a dakatar da rantsarwar tare kuma da kirkiro wasu masarautu, amma wasu rahotanin sun nuna cewar gwamnatin jihar ta ce bata sami takardar umarnin Kotun ba.

More News

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...

Wata mata ta mutu bayan da kwantena ta faÉ—o kan motar da take ciki

Wata kwantena mai tsawon ƙafa 40 dake maƙare da kaya ta faɗo kan wata ƙaramar mota ƙirar Nissan mai rijistar namba ABJ 692 BG...

Kotu ta bayar da belin Emefiele bayan ya cika sharuÉ—a

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele bayan da ya cika dukkanin sharudan beli da kotun ta gindaya. Emefiele...

Kotu ta É—aure Bobrisky wata shida a gidan yari

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas, a ranar Juma’a, ta yanke hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso wa Idris Olarewaju...