Ya kamata a kafa kwamitin da zai binciki ibtila’in bam a kauyen Kaduna, a kuma biya diyya—in ji Sheikh Ɗahiru

Biyo bayan harin bam da aka kai a kauyen Kaduna a wajen bikin Mauludi, malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya roki gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta kafa kwamitin bincike cikin gaggawa.

A cewarsa, gudanar da cikakken bincike kan tashin bama-bamai na da matukar muhimmanci wajen dakile irin wannan da kan iya faruwa a nan gaba ta hanyar nazarin yanayin da ya haifar da wannan musiba.

Babban malamin addinin Musuluncin kuma jagoran mabiya darikar Tijjaniyya ya yi kira ga gwamnati da ta biya diyya ga iyalan da harin bam ɗin ya rutsa da su a garin Tundun Biri na jihar Kaduna bisa kuskure.

Da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi, ya bukaci gwamnatin shugaba Tinubu da ta tabbatar da an yi adalci ga wadanda abin ya shafa tare da hana afkuwar lamarin nan gaba ta hanyar hukunta masu laifi.

More from this stream

Recomended