Ya kamata ƴan Najeriya su rika addu’a kan kashe-kashen da ake fama da shi—CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’a kan kashe-kashen da ake yi a kasar nan tun shekarar 2023.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, a sakonsa na sabuwar shekara da ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana rashin jin dadinsa kan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa rayuka sama da 200 a jihar Filato, yana mai cewa ya kamata ‘yan Najeriya su rungumi bambancin al’ummar kasar.

Okoh ya ce ya kamata ‘yan kasar su bar bambance-bambancen kasar su zama ginshikin da za a gina kasa mai karfi da jituwa a tsakanin juna.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...