
Gwamnatin jihar Lagos ta ce masallatai da kuma majami’u za su cigaba da zama a rufe duk da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na sassauta dokar da ta hana bude wuraren ibada.
Da yake magana da yan jaridu a ranar Talata, Kwamishinan harkokin cikin gida, Alofiu Elegushi ya ce bude wuraren ibada a yanzu ba zai yiyu ba saboda jihar ce cibiyar cutar Korona a Najeriya.
Lagos na da mutane 5135 da suka kamu da cutar.
Kwamishinan ya ce gwamnati ta gudanar da tarurruka da dama da shugabannin addini inda suka amince cewa baza a bude wuraren ibada ba har sai komai ya fara dawowa dai-dai.
A taron shugabannin addinan sun tabbatarwa da gwamnati cewa baza su iya tabbatar da kayyade mutanen da za su halarci wuraren ba.