Wolfsburg ta raba gari da Georges Ntep na Kamaru

Paul Ntep

Kungiyar Wolsburg da dan kwallon tawagar Kamaru Paul-Georges Ntep sun amince kowa ya kama gabansa.

Dan wasan mai shekara 27, bai samu damar buga wasa akai-akai ba a Jamus, inda ya buga karawa 19 a Wolsburg tun da ya coma can a 2017 daga Rennes.

Ntep ya buga wasannin aro a zango na biyu a 2018/19 a kungiyar Saint-Etienne ta Faransa.

Haka kuma a kakar nan ya taka leda aro a Turkiya a tare da Kayserispor wadda ta amince za ta saye shi, amma matsalar rashin kudi ya sa aka hakura da cinikin.

Yanzu haka Ntep na neman kungiyar da zai buga wa tamaula domin ya samu gurbin buga wa tawagar Kamaru gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta karbi bakunci a 2021.

Ya buga wa matasan Faransa masu kasa da shekaru har mataki hudu tun daga ‘yan 18 zuwa 21, ya kuma buga wa babbar tawagar wasannin sada zumunci biyu, daga baya ya koma yi wa Kamaru wasa a 2018.

Tun da ya amince da buga wa Kamaru kwallon kafa ya ci kofi hudu a Indomitable Lions ya kuma buga wasa biyu karkashin Clarence Seedorf.

More from this stream

Recomended