
Asalin hoton, AFP
Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince a fara gwada magungunan yaki da cutar korona na gargajiya da aka samar a Afirka.
Cikin wata sanarwa, ofishin hukumar na Afrika dake a Brazzaville ya ce ya amince da yarjejeniyar gwada magungunan dai-dai da sauran gwaje-gwajen da ake yi wa rigakafin cutar da ake samarwa a kasashen duniya.
Hukumar ta ce duk wani maganin gargajiya da aka yanke hukuncin na da inganci to kuwa za a iya fara amfani da shi a fadin duniya.
Hukumar ta ce tantance magungunan ta ingantacciyar hanyar kimiyya ce za ta fayyace ingancin magungunan gargajiya da za su taimaka wajen yaki da cutar ta korona.
Asalin hoton, AFP
Matakin ya zo ne watanni bayan da shugaban Madagaska ya shelantawa duniya wani maganin gargajiya da ba a gwada ba, da yace zai taimaka wajen dakile cutar ta korona.
Shugaban ya fita cikin gari yana raba wa al’ummarsa maganin tare da kayan masarufi kamar shinkafa da man girki da siga ga marassa galihun cikinsu a Antananarivo babban birnin Æ™asar.
Kawo yanzu babu wata hujjar da aka fitar da ke nuna cewa maganin na aiki – amma mutanen Afirka da dama na nuna shi a matsayin wani abin alfahari da nahiyar ta samar.
Suma wasu kasashe kamar Tanzania, da Comoros, Guinea-Bissau da Congo duk sun samar da nasu magungunan gargajiyan da ba a gwada ba.