Watakila Madrid ta lashe La Ligar bana ranar Alhamis

Real Madrid

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Real Madrid na bukatar maki biyar nan gaba ta lashe kofin La Liga na bana, kuma karon farko tun kakar 2016-17.

Bayan da Real ta doke Alaves ranar Juma’a, hakan ne ya kara haska fitalar cewar kungiyar ta dauko hanyar cin kofin La Liga na bana.

Saboda haka Madrid na bukatar cin wasa daya da canjaras nan gaba ta lashe kofin bana, wanda ya ci karo da cikas cikin watan Maris, saboda bullar cutar korona.

Ko kuma za ta iya rashin nasara a wasa daya daga ukun da ke gabanta, sannan ta cinye sauran biyun, nan ma za ta dauki kofin La Liga na shekarar nan.

Watakila ko sai a wasan karshe a tantance zakara, idan Real ta yi sakaci, koda yake a Spaniya ana amfani da wanda ya ci wani a haduwa a La Liga, maimakon wadda keda yawan rarar kwallaye a wasu gasar Turai.

Da zarar Real Madrid ta yi nasara a karawar mako na 36 da za ta buga da Granada ranar Litinin, to za ta iya lashe La Liga kenan idan ta doke Villareal ranar Alhamis.

A kuma ranar Barcelona za ta fafata da Osasuna a karawar mako na 37 a kakar bana, da zai rage saura wasa daya a karkare La Liga.

Sai dai da zarar Real Madrid ta bari an doke ta a wasa uku na gaba, kuma Barcelona ta hada maki shida to lallai kam lissafi zai canja, inda Barca za ta ci La Liga na uku a jere kenan,

Real Madrid za ta buga wasan karshe na mako na 38 da Leganes ranar 19 ga watan Yuli da kungiyar da ake ganin za ta bar wasannin bana zuwa karamar gasar Spaniya,

A kuma ranar Barcelona za ta ziyarci Deportivo Alaves a wasan karshe na mako na 38 a La Liga.

Bayan da Barcelona ta buga wasan mako na 36 ta hada maki 79 a mataki na biyu, Real Madrid ce ta daya a kan teburi tana da maki 80 a wasa 35 da ta buga a La Liga.

Real Madrid tana da kofin La Liga 33 jumulla, ita kuwa Barcelona tana da 26 kawo yanzu.

More News

An ji ƙarar harbe-harbe a fadar Sarkin Kano

A daren ranar litinin ne aka bayar da rahoton jin harbin bindiga a kusa da karamar fadar inda hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero,...

Ministan shari’a nason INEC ta riƙa shirya zaɓen ƙananan hukumomi

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya yi kira da a soke hukumar zaɓen jihohi masu zaman kansu. Da yake magana a...

Kotu ta hana Aminu Ado ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Babbar Kotun jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero ayyana kansa a  matsayin Sarkin Kano har sai ta kammala sauraron ƙarar dake gabanta. Kotun ta...

NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya haɗiye ƙunshi 111 na hodar ibilis  a filin jirgin saman Abuja

Jami'an Hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Orjinze wani ɗan kasuwa akan...