Wata motar tanka dake ɗauke da iskar gas ta kama da wuta akan gadar sama ta Obiri-Ikwere dake kan titin East-West a birnin Fatakwal na jihar Ribas.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa motar ta ci karo da wani abu ne inda ta kifa ta kuma yi bindiga nan take wuta ta kama.
An ji ƙarar fashewar da motar tayi a wurare dake da nisa sosai daga inda lamarin ya faru.
Jami’an hukumar kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar bayan da suka yi gaggawar zuwa wurin akan lokaci.
Kawo yanzu bai a bayyana mutane nawa ne suka rasu ko kuma suka jikkata sakamakon fashewar.