Wata motar shanu ta yi hatsari a Kano

Wata babbar mota dake ɗauke da shanu da dabbobi da za akai Enugu ta hantsila akan gadar sama dake kan titin Maiduguri a jihar Kano.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa motar na ɗauke da shanu 28, tinkiyoyi da kuma albasa.

Ɗaya daga cikin fasinjojin dake cikin motar mai suna Hashimu Rabi’u Tamburawa ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa motar ta baro Wudil domin zuwa Enugu amma bayan da suka isa gadar saman dake Hotoro sai kawai ta tuntsura.

Ya ce wataƙila shanyewar birki ne ya jawo hatsarin.

Jami’an ƴan sanda da na hukumar kiyaye afkuwar haɗura da kuma na hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun garzaya wurin domin kai ɗaukin gaggawa.

An kai waɗanda suka jikkata asibitin Sir Sanusi dake unguwar Ƴan Kaba.

Kawo yanzu ba a samu asarar rayuka ba a hatsarin.

More from this stream

Recomended