Wata Mata Ta Watsa wa Mijinta Ruwan Zafi Saboda Yaƙi Zuwa Da Ita Bikin Abokinsa

Rundunar yan sandan jihar Lagos ta ce wata mata mai suna, Dorcas Oluwabukola ta shiga hannun yan sanda bayan da aka zargeta da watsawa mijinta ruwan zafi biyo bayan sabani da suka samu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN.

Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne ranar 18 ga watan Disamba.

Ya ce wacce ake zargin ta tafasa ruwan zafi ta watsawa mijin nata kan zargin cewa yaki zuwa da ita wurin bikin abokinsa.

Ya kara da cewa a ranar ne aka kama matar bayan sa ofishin yan sanda na Meiran ya samu labarin faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended