Wata mata ta mutu bayan da kwantena ta faɗo kan motar da take ciki

Wata kwantena mai tsawon ƙafa 40 dake maƙare da kaya ta faɗo kan wata ƙaramar mota ƙirar Nissan mai rijistar namba ABJ 692 BG inda ta kashe wata mata nan take.

Mummunan hatsarin ya faru ne a yankin NNPC dake Alepere a jihar Lagos.

Direban motar tare da yaronsa sun samu nasarar tserewa dan gudu kada ɓata gari  su farmusu.

Matar da mutu na zaune ne a kujerar baya ta motar a yayin da direban ya samu tsira da ransa ba tare da ko ƙwarzane ba

Tuni aka kai gawar matar dakin ajiye gawarwaki.

Adebayo Taofiq daraktan sashen hulɗa da jama’a na hukumar sufuri ta jihar Lagos LASTMA ya tabbatar da faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended