
Wata kungiya mai zaman kanta dake Abuja ta jagoranci zanga-zangar nuna goyon baya ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC kan matakin da ta dauka game da jam’iyar adawa ta ADC.
Kungiyar mai suna Concern Nigerian Youth Forum ta gudanar da zanga-zangar ne a ofishin hukumar ta INEC dake Abuja.
Shugaban kungiyar Adeyeye Olugbenga ya ce sun gudanar da zanga-zangar domin kare da dimakwaradiya da kuma mutuncin hukumar ta INEC.
Ya ce zanga-zangar ta zama dole duba da yadda hukumar INEC ke fuskantar suka daga wasu mutane tun bayan da ta aiwatar da hukuncin kotu da ya soke shugabancin jam’iyar ta ADC.


