Wata kotu a Afghanistan ta bulale wata budurwa saboda haramtacciyar soyayya


Wata kotun Taliban a lardin Faryab na arewacin Afghanistan ta yi wa wata mace bulala 30 a gaban jama’a tare da yanke mata hukuncin watanni shida a gidan yari saboda yin dangantakar haram da kuma guduwa daga gida.

A cewar sanarwar da Babban Kotun Taliban ta fitar a ranar Litinin, an yanke wa matar hukunci ne bisa karya dokokin Afghanistan da ke hana dangantaka ta jima’i a waje da aure.

A wani lamari daban, mutane biyu a lardin Kandahar da ke kudancin kasar sun sha bulala 30 a gaban jama’a tare da hukuncin shekara guda a gidan yari bisa laifin aikata luwaɗi.

Dawowar Taliban mulki a Afghanistan ta kawo ƙaruwar aiwatar da hukunci irin na kisa da bulala a bainar jama’a, musamman ga laifukan kisan kai, fashi da makami, da zina.

Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta yi kakkausar suka ga amfani da hukuncin bulala da Taliban ke yi, tana mai cewa hakan ya sabawa yarjejeniyar MDD kan hana azabtarwa.

UN ta yi kira ga Taliban da su daina amfani da irin waɗannan hukunci.

Amma hukumomin Taliban sun kare matakan nasu, suna cewa hukuncin bulala ya yi daidai da dokokin Afghanistan kuma yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron al’umma.

More from this stream

Recomended