Mutane da dama ne suka tsallake rijiya da baya bayan da wata babbar mota dake dauke da madarar gari ta fada kan wani Masallaci a garin Suleja dake jihar Neja.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 bayan da mutane suka fice daga jim kaɗan bayan kammala sallar Asubahi.
A cewar shedar gani da ido motar ta fada bayan masallacin ne inda mata da yara suke sallah.
Amma kuma mutane uku sun jikkata ciki har da yaro guda.