Wataƙila a buɗe iyakar Najeriya da Kotono

Masu jigilar kaya da ke aiki a iyakar Seme sun rubutawa gwamnatin tarayya wasika suna bukatar a bude kan iyakoki domin shigo da motoci.

Daraktan Sufuri na Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Ibrahim Musa ne ya bayyana haka a Seme yayin wani taro tsakanin jami’an Najeriya da Benin da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta shirya.

Ya bayyana cewa masu jigilar kayayyaki sun yi kira ga tsohon karamin ministan sufurin jiragen sama a ziyararsa ta karshe da ya kai kan iyakar, inda ya nemi a sake farfado da iyakar.

Ya ce takardar da aka shirya aka aika zuwa ga gwamnatin tarayya bisa wannan bukata majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da ita.

More from this stream

Recomended