
Adamu Bulkachuwa,sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa a majalisar dattawa ya ce da yawa daga cikin abokan aikinsa na jam’iyyar su ta APC sun goyi bayan yunkurin tsige shugaban kasa, Muhammad Buhari.
A makon da ya wuce ne sanatocin da suka fito daga jam’iyyar PDP da wasu jam’iyun adawa suka bawa shugaban kasar wa’adin mako 6 kan ya shawo matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
Da yake magana a gidan talabijin na Channel a ranar Litinin, Bulkachuwa ya ce barazanar tsigewar ita ce mataki na karshe da ya zama dole yan majalisar su dauka.
Ya ce shi da abokan aikinsa sun gwada taimakawa bangaren zartarwa dama shi kansa shugaban kasa ta hanyoyi da dama domin magance matsalar tsaro a kasarnan amma abin ya ci tura.