
Wasu mutane da ba a san ko suwaye ba sun nemi halaka wata matar aure bayan da suka daure ta da igiya.
Lamarin ya faru ne a unguwar Gaida Geza dake karamar Hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
Wasu dake wuce wa ne suka ji wo kakarin matar inda suka ankarar da makota aka shiga aka tarar da ita cikin wani yanayi.
Tuni mazauna yankin suka sanar da rundunar yan sanda faruwar lamarin sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga rundunar yan sandan jihar Kano.