Wasu Mazauna Birnin Kebbi Sun Wawushe Kayan Abinci A Rumbun Ajiyar Gwamnati

Wasu mazauna jihar Kebbi sun kai farmaki rumbun ajiye kayan abinci na gwamnati dake yankin Bayan Ƙara a Birnin Kebbi  a daren ranar Asabar inda suka sace kayan abinci.

Ɓatagarin wanda suka fi ƙarfin jami’an tsaro da aka a jiye a wurin ajiye kayayyakin sun kuma farfasa wasu wuraren ajiyar kayayyaki da kuma shaguna na mutane inda suka yi musu satar kayan abinci.

Sun kuma sace kayan abinci dake cikin wata mota da ta lalace wanda za a rabawa mutane a birnin Kebbi.

Hare-hare kan ɗakunan ajiye kayan abinci ya faru a garin Suleja dake jihar Niger da kuma babban birnin tarayya Abuja..

Da yake magana da wakilin jaridar Daily Trust shugaban kungiyar masu sayar da kayan abinci a kasuwar ta Bayan Kara dake birnin Kebbi ya ce matasan sun ƙone shaguna da kuma wuraren ajiye kayan abinci.

“Su jami’an tsaro sun yi harbin iska da kuma na barkonon tsohuwa amma su matasan ba su tsorata ba sai da suka kutsa kai suka kwashe kayan abincin dake rumbun  a jiyar gwamnati da kuma wasu daga cikin shagunan mu.”

Related Articles