Wasu matasa guda uku sun bayyana a gaban wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Gyadi-Gyadi dake Kano inda ake tuhumarsu da zargin yin garkuwa da mutane.
Ana zarginsu ne da yin garkuwa da Muhammad Nasir wani yaro mai shekaru 4 kuma suka buƙaci a biya su dala $180 a matsayin kuɗin fansa..
Amma kuma jami’an tsaro suka bi diddiginsu suka kama su.
Waɗanda ake zargin Hizbullah Salisu, Aliyu Abubakar da kuma Hassan Aliyu an tuhume su da laifin haɗabaki, aikata laifi da kuma yin garkuwa da mutum.
Alƙaliyar kotun Rakiya Lami Sani ta bada umarnin a tura su gidan gyaran hali bayan da suka ƙi amsa laifin da ake tuhumarsu.