Wasu masu garkuwa da mutane  sun tuba a jihar Taraba

Wasu masu garkuwa da mutane Gayya Alhaji Abdu da kuma Siyyo Alhaji Amadu sun tuba inda suka miƙa kansu ga shugabannin kungiyar mafarauta ta jihar Taraba inda suka ce ƙashin kansu suka dena yin garkuwa da mutane.

Gayya ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa sau biyu ana zuwa garkuwa da mutane da shi inda ya ce an bashi ₦200,000 a kowanne bayan da waɗanɗa aka yi garkuwa da su suka biya naira  miliyan biyar kowannensu.

Gayya ya ce ya shiga garkuwa da mutane bayan da ya gano cewa sunansa na cikin mutanen da ake nema za a kama da laifin garkuwa da mutane duk da cewa bai taɓa aikata wani laifi ba ballantana kuma yin garkuwa da mutane. Shi ya sa ya gudu daga gidansu saboda yasan idan aka kama shi za a iya kashe shi.

Ana sa bangaren Amadu ya ce a ƙashin kansa ne ya shiga gungun masu yin garkuwa da mutane a yankin Mayo-Renewo dake ƙaramar hukumar Arɗo Kola.

Ya faɗawa wakilin jaridar cewa an yi garkuwa da mutane da dama tare da shi kafin ya yanke shawarar ya tuba.

Babangida Kwamando, shugaban mafarautan ya ce a ko da yaushe yana karɓar ƴan fashin daji da kum masu garkuwa da mutane da suka tuba suka kawo kansu.

Ya ƙara da cewa masu garkuwar da kuma ƴan fashin dajin sukan rantse da alƙur’ani cewa baza su kara yi ba.

More from this stream

Recomended