Wasu Mahajjatan bana sun kai ziyara Kogon Hira da ke a Makkah a ƙasar Saudi Arabia.
Kogon Hira dai shi ne wuri na farko da Annabi Muhammad S.A.W ya karbi wahayi.
Za a fara aikin hajjin bana ne dai a mako mai zuwa inda ake sa rai fiye da mutum miliyan biyu za su sauke farali.