
Jam’iyar PDP a ranar Alhamis ta gudanar da taron gangamin yakin neman zabe a jihar Osun gabanin zaɓen gwamnan jihar gwamnan jihar da za ayi.
Za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.
An gudanar da taron yakin neman zaben ne a Osogbo babban birnin jihar inda jam’iyar ta bukaci a zabi dan takarar ta Ademola Adeleke.
Taron gangamin ya samu jagoranci ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar da kuma shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Abubakar Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto,Aminu Waziri Tambuwal, na Bayelsa,Douye Diri, Godwin Obaseki na Edo, da kuma Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
Sai dai wasu daga cikin gwamnonin jam’iyar sun kauracewa taron kamar na jihar Rivers,Nyesom Wike, Samuel Ortom na jihar Benue, Seyi Makinde na jihar Oyo, Ikpeazu Okezie na jihar Abia da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.
Ana ganin dai kauracewar ta su nada nasaba da rikicin da ya biyo bayan zaɓen mataimakin shugaban kasa da Atiku Abubakar yayi.