Wasu daga cikin sabbin gwamnoni da suka kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu da kuma wasu da suka sauka a ranar sun kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ziyara a gidansa dake Daura a jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Garba Shehu ya fitar ya ce gwamnonin sun kai ziyarar ne domin godewa tsohon shugaban kasar.
Buhari ya gode ma su bisa ziyarar kana ya kuma tunatar da su irin nauyin da yake kansu.