Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.

An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating Base Dansadua domin aikin Operation Fansan Yamma, inda ake zargin ya kashe abokin aikinsa a wani yanayi mai cike da tambayoyi.

Lamarin ya faru da sanyin safiyar Juma’a a jihar Zamfara.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Daraktan Ayyukan Watsa Labaran Tsaro, Manjo Janar Buba Edward, ya ce sojan ruwan ya harbi abokin aikinsa sau da dama.

Buba ya ce, “A ranar 25 ga Oktoba, 2024, da misalin karfe 3:12 na safe, wani jami’in sojan ruwa, LS Akila A., wanda aka tura zuwa FOB Dansadua domin Operation FANSAN YAMMA, a wani yanayi mai cike da tambayoyi, ya bude wuta ba kakkautawa ya kashe abokin aikinsa.

“Daga nan aka kama shi, aka kwace masa makami, aka kuma tsare shi, kuma bincike ya fara kan lamarin. Bayan kammala bincike, za a mika shari’ar a gaban kotun soji da aka tanada domin magance irin wadannan laifuka a tsakanin dakarun tsaro.”

More from this stream

Recomended