Wani soja ya harbe kansa har lahira a jihar Ogun

Wani sojan rundunar sojan Najeriya, ya kashe kansa a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Sojan mai suna, Boyi Thankgod yana aiki ne da Atileri birget ta 35 dake Alamala a Abeokuta babban birnin jihar ta Ogun.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa sojan ya harbe kansa ne a wurin bikin tunawa da yan mazan jiya da aka gudanar.

Wani hoto marar dadin kalla ya nuna gawar marigayin kwance cikin jini yayin da kansa ya fita daga gangar jikinsa saboda karfin harbin bindigar.

“Kwarai gaskiya ne lamarin ya faru jiya ranar ( Litinin) ” kamar yadda wata majiya dake barikin ta fadawa jaridar Daily Trust.

Majiyar ta ƙara da cewa ana cigaba da bincike domin gano dalilin da yasa sojan ya kashe kansa.

More from this stream

Recomended