Babbar kotun tarayya dake zamanta a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom ta aike da Sanata Bassey Akpan shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hako bangaren hako man fetur ya zuwa gidan yari.
Hukuncin kotun ya nuna cewa sanata Akpan zai shafe shekaru 42 a gidan yari bayan da aka same shi da aikata cin hanci da rashawa.
Hukumar EFCC dake yaki da ma su yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ita ce ta gurfanar da shi a gaban kotun.
Kotu ta samu Akpan da laifin karbar cin hancin motoci 12 da kudinsu ya kai miliyan 254 daga hannun wani dillalin man fetur mai suna Olajide Omokore lokacin da yake kwamishinan kudi na jihar Akwa Ibom daga shekarar 2010 zuwa 2014.