Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa zargin kashe mahaifiyarsa mai suna Aminat, wadda aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya, biyo bayan wata takaddama kan kudin da aka sayar da kwakwar manja.
Wani ganau mai suna Rasaki ya shaida a ranar Lahadi cewa Lukman da mamaciyar sun dauki wani lebura ne wanda ya taimaka musu wajen sayar da wasu ƴaƴan kwakwar.
Yayin da ma’aikaciyar ke son mika kudin, an ruwaito marigayiya Aminat ta dage cewa sai an ba da kudin ta hannunta, lamarin da ya harzuka ɗan nata.
Ya ci gaba da cewa, “Mutanen kauyen duk sun ji takaici da muka samu labarin faruwar lamarin. Lamarin ya faru ne a kauyen Kajola da ke kusa da Apomu ranar Asabar da misalin karfe hudu na yamma.”