Wani mutumi a Katsina ya yaye bugun kwanon gidansa don biyan kuɗin fansa

0

Kunci ya kai wani mutumi a Katsina maƙura saboda matsi ya kai shi har bugun kwanon gidansa ya yaye zai sayar saboda biyan kuɗin fansa bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗansa

Mutumin mai suna Sa’idu Faskari shi ma ya taɓa shiga hannun ƴan bindigar a watan Disamba, inda sai da aka biya dubu hamsin kafin ya kubuta daga hannunsu.

A wajen karɓo shi ne, bayan ɗansa ya kai masu kuɗin fansa don karbarsa ne, kuma suka damƙe shi ɗan.

Ga shi yanzu suna buƙatar dubu 100 suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here