Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.

Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Filato ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Jos.

Mista Dauda ya ce marigayin wanda ya fito daga karamar hukumar Mangu ta jihar ya rasu ne a ranar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.”

Ya yi rashin lafiya kuma tun ranar 31 ga watan Mayu yake jinya a Asibitin kwararru na Annur da ke Makka.

“Muna so mu mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, gwamnati da jama’ar Filato.

“Muna addu’ar Allah ya karbi aikin hajjinsa, ya ba shi hutu na har abada, ya kuma baiwa iyalansa karfin gwiwar jure wannan babban rashi,” inji Mista Dauda.

More from this stream

Recomended