Wani mahaifi ya yi wa ‘yarsa mai shekaru 13 ciki

Wani mutum dake da matsakaitan shekaru ya shiga hannun jami’an tsaro bayan da aka zarge shi da yiwa yarsa mai shekaru 13 fyade har ta kai ta samu juna biyu.

Mutumin da ake zargi mai suna, Friday Moses na daga cikin mutane 72 da kwamishinan Æ´ansandan jihar Edo,Johnson Babatunde Kokumo ya bajekolinsu ga manema labarai bisa zargin da ake musu na aikata laifuka daban-daban a jihar.

Kokumo ya ce an kama sune bisa zargin aikata laifuka da dama da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade da kuma shiga kungiyoyin asiri.

Ya ce da yawa daga cikin mutanen da ake zargi sun kasance É—alibai, ya yin da ragowar kuma bata gari ne da suke shigowa jihar domin aikata laifuka.

Kokumo ya tabbatar da cewa za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Rundunar ta gano cewa Moses wanda dan asalin jihar Cross River ne amma yana zaune a Edo ya dade yana aikata lalata yar tasa tun tana yar shekara 7.

Yarinyar dake aji shida na makarantar firamare ta rasa mahaifiyar ta shekaru 5 da suka wuce kuma tun daga wancan lokacin ne mahaifinnata ke cin zarafin ta.

Lokacin da al’ummar unguwar da yake zaune suka gano yarinyar na dauke da cikin mahaifiyarta sun sanar da jami’an tsaro har ta kai ga an kama shi.

Da take wa yan jarida jawabi yarinyar wacce aka ce na dauke da ciki dan wata biyar ta ce mutumin da ake zargi ya dade yana lalata da ita tun lokacin da take yar karama.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...