Wani jami’in kwastam ya harbe kansa har lahira a Kano

Wani jami’in hukumar kwastam ya harbe kansa har lahira a gidansa dake unguwar Farm Centre a cikin birnin Kano.

Mai magana da yawun rundunar Æ´an sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kiyawa ya ce jami’in mai suna Abdullahi Magaji na aiki ne a hedkwatar hukumar ta kwastam dake Abuja ana zargin cewa ya kashe kansa ne a ranar 06 ga watan Mayu.

Babban baturen Æ´an sanda na Farm Centre shi ne ya jagoranci jami’an Æ´an sanda ya zuwa gidan da abun ya faru.

Tuni dai kwamishinan Æ´an sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...