Dantakarar jam’iyar APC kuma gwamna mai ci, Hope Uzodimma ya sake lashe zaɓen gwamnan da aka yi a ranar Asabar.
Uzodimma ya samu nasara ne da gagarumin rinjaye kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar ya nuna.
Gwamnan ya samu nasara da kuri’a 540,308 akan manyan abokanan takararsa na jam’iyar PDP da Labour Party.
Sakamakon ƙananan hukumomin jihar 27 da INEC ta bayyana ya nuna cewa gwamnan ya lashe zaɓen da a dukkanin kananan hukumomin.
Jam’iyar PDP ce tazo ta biyu a zaɓen da kuri’a 71,503 sai kuma jam’iyar Labour Party inda ɗan takararta Athan Achonu ya samu kuri’a 64,081.