Uwar Jam’iyar APC ta naɗa magoya bayan Nyesom Wike shugabancin jam’iyar a jihar Rivers

Jam’iyar APC ta rushe shugabancin jam’iyar na jihar Rivers inda ta naɗa kwamitin riƙo mai wakilai 7 da zai cigaba da jagorancin ragamar shugabancin jam’iyar.

Jam’iyar APC a jihar ta Rivers ta shafe shekaru da dama tana fama da rikici.

Sai dai kuma kwamitin riƙon jam’iyar da aka naɗa yanzu na cike ne da mutanen dake biyayya ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike wanda shi ne ministan birnin tarayya Abuja.

Da yake magana da manema labarai a Abuja, mai magana da yawun jam’iyar APC na kasa, Felix Morka ya ce kwamitin riƙon zai kasance ƙarƙashin Cif Tony Okocha tare da Cif Eric Nwibani a matsayin shugaban da sakatare.

A ranar Juma’a ne za a rantsar da kwamitin inda hakan ke nuna cewa yanzu jam’iyar ta tashi daga hannun tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

More from this stream

Recomended