Ubang: Kauyen da mata da maza ke magana da harshe daban-daban

[ad_1]

Ubang wani kauye ne da ake rike da al'ada

Image caption

Ubang wani kauye ne da ake rike da al’ada

A kauyen Ubang, wani karamin garin masunta a kudancin Najeriya, maza da mata sun ce suna magana da yaruka daban-daban.

Suna ganin wannan bambancin na al’ummarsu a matsayin “wata baiwa daga Allah”, amma yayin da ake samun karin matasa dake fita neman aiki a wajen garin, kuma turancin Ingilishi yake dada samun karbuwa, ana fargabar cewar harsunan ba za su dore ba, kamar yadda wakiliyar BBC Yemisi Adegoke ta ruwaito.

Yayin da yake sanye da tufafi mai haske da jar dara ta basarake, kuma yake rike da sanda a ahannunsa, Cif Oliver Ibang ya kira ‘ya’yansa biyu domin ya nuna yaruka biyun.

Ya daga doya sannan ya tambayi ‘yarsa me ake kiransa.

Ta ce “‘irui’ ne,”, ba tare da wani tunani ba.

Amma a “yaren maza” na kauyen Ubang kalmar doya , daya daga cikin abin da aka fi ci a Najeriya, ita ce “itong”.

Kuma akwai misalai masu yawa, kamar kalmar da ake amfani da ita wajen kiran tufafi, wanda maza ke kira “nki” kuma mata ke kira “ariga”.

Babu tabbacin adadin kalomin da suke bambanta a harsunan guda biyu kuma babu salon yadda ake yawanta amfani da kalmomin ko sun ada alaka da irin gudumawar maza ko mata.

“Kamar harsuna daban-daban suke,” in ji masanin nazari kan dan Adam Chi Chi Undie, wanda ya yi nazari kan al’ummar.

“Akwai kalmomi da maza da mata suke mafani da su tare, kuma akwai wasu wadanda suka bambanta dangane da jinsin mutum. Furucinsu ba daya ba ne, harrufansu b adaya ba ne, kalomi ne daban-daban.”

Alamar girma

Ta ce bambance-bambancen sun fi wadanda ke tsakanin, alal misali, turancin Ingilashi na Birtaniya da na Amurka.

Duk da haka , maza da mata za su iya fahimtar juna da kyau -ko kuma yadda za a iya samu a ko ina a duniya.

Image caption

Cif Oliver Ibang yana son ya gina cibiyar raya harshe domin nuna al’adar Ubang wadda ta fita daban

Wannan ka iya kasancewa saboda yara maza suna girma da yaren mata , domin sun fi dadewa da iyayensu mata da sauran mata a lokacin da suka kananan yara, kamar yadda Chif Ibang ya bayyana.

A lokacin da suka kai shekara 10, ana tsammain yara maza su yi magana da “harshen maza”, in ji shi.

“Akwai matakin da namiji zai kai kuma zai gane cewar ba ya amfani da harshen da ya kamata. Babu wanda zai gaya mishi ya sauya zuwa yaren maza.”

“A lokacin da ya fara magana harshen maza , zaka san girma ya fara zuwa masa.”

Idan yaro ko yarinya ta ki koma amfani da harshen da ya kamata a lokacin da shekrunsa suka kai wani mataki, ana ganin suna da “matsala”,in ji shi.

Mutanen Ubang suna alfahari da bambance-bambancen harsunansu kuma suna ganisa a matsayin abin da ya sa ya fita daban.

Amma akwai bayanai daban-daban game da yadda harshen ya samu asali. Yawancin mutanen kauyen sun bayar bayani mai alaka da baible.

“Allah Ya halicci Adam da Hauwa’u, kuma mutanen Ubang ne ,” in ji cif din.

Ya ce Allah Ya yi shirin bai wa ko wane yare harsuna biyu ne , amma bayan ya hallici yaruka biyu wa mutanen Ubang, sannan ya ga yarukan ba za su ishi ko wane yare ba.

“Saboda haka ya dakatar (da raba harsunan). Sabodahaka ne Ubang take da yaruka biyu – mun bambanta daga sauran mutanen duniya.”

Al’adar jinsi biyu

Mis Undie tana da bayani na nazarin tarihin dabi’ar dan Adam.

“Wannan al’ada ce ta jinsi biyu,” in ji ta.

“Maza da mata suna harkokinnsu a kusan wurare biyu daban-daban. Kamar suna cikin duniya biyu ne daban-daban, amma wadannan duniyoyin sukan haduwa a wasu lokutan kuma za ka wannan salon a yaren ma.”

Image caption

Ana hana yaran Ubang magana da harshensu a makaranta

Ta ce bayaninta bai bayar da dukkan amsoshinba.

“Ina kiransa cikakken nazariu (theory) amma yana da rauni,” in ji ta. “Domin a Najeriya a kwai ababen da suka jibinci jinsi biyu kuma ba mu da irin wannan al’ada na harshen.”

Ana fargaba game da dorewar harsunan.

Ba a rubuta yaren maza da na matan ba. Soboadahaka makomarsu ta dogara ne game yadda yara suka mika yarukan ga wadanda za su zo bayansu. Amma a wannan zamanin matsa kadan ne suke iya daya daga cikin harsunan da kyau.

“Ina ganinsa da matasa,” in ji malamin makarantan Sakandare, Steven Ochui.

“Da wuya su iya magana da harsunan Ubang ba tare da sun hada da kalmar turancin Ingilshi ba.”

Aibanta harshen uwa

Wannan ya nuna abin da ke faruwa a fadin Najeriya.

A shekarar 2016 kungiyar masana harshe ta Najeriya ta ce 50 daga cikin harsuna 500 kasar za su iya bata cikin ‘yan shekaru kadan idan ba a dauki muhimmin mataki ba.

Harsunan Yoruba da Igbo da Hausa su ne manyan harsunan Najeriya, tare da Ingilishi -wadda a ke amfani da ita domin hadin kai a kasar da ke da yaruka da yawa.

Image caption

Daliba Stella Odobi tana fargabar cewar iyaye ‘yan kabilar Ubang ba sa koya wa ‘ya’yansu harsunansu

Ana koyar da manyan harsunan a makaranti a fadin kasar domin bin manufar ba da ilimi ta kasar wadda takje magana kan bukatar raya al’ada.

Ita manufar ta kuma ce “ko wane yaro/yarinya zai koyi harshensa”.

Amma ba a dabbaka wannan a Ubang, inda ake hana yara tare da hukunta yaraidan suka yi magana da yarensu a makaranta.

Mista Ochui ya ce yana fargaba game da tasirin “aibanta” harshen uwa domin bai wa dalibai kwarin gwiwar magana da Ingilishi.

“A makarantarmu a nan muna hukunta dalibai – muna dukan su, a wasu lokutan suna biyan tara -domin sun yi magana da harshen mahaifiyarsu,” in ji shi.

“Idan ka dakji yaro domin ya yi magana da harshensa. harshen ba zai dre ba.”

Ana bukatar littatafai

Mista Ochui ya ce ana bukatar a kara hobbasa wajen ceto harsunan Ubang.

“Muna bukatar littatafan karatu da aka rubuta da harsunan Ubang -littatafan kagaggun labarai (novels) da zane-zane da kuma fina-finai – kuma su ba mu damar koyar da harssunan a makaranti,” in ji shi.

Stella Odobi,wata daliba a Ubang, ta yarda ana bukatar kara kokari wajen ceto harsunan daga mutuwa.

“Iyaye suna kai yaransu su je su yi karatu a kauyuka daban-daban kuma ba sa damuwa su su koya musu harsunan iyayensu,”in ji ta.

Amma ta ce tana daga cikin matasa da yawa a cikin kauyen wadanda suke da niyyar koya wa ‘ya’yansu harsunan Ubang ko ma sun bar kauyen.

Cif Ibang yana fatan cewar wata rana za a kafa cibiyar raya harshe a Ubang, wanda zai nuna yadda harsunan garin suka fita daban.

Kuma yana da kwarin gwiwar cewar harsunan za su dore.

“Idan harsunan suka mutu , mutanen Ubang za su kare.”

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...