Uba Sani ya bayar da umarnin yin bincike kan harin soja da ya kashe mutane 30

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba sani ya bayar da umarnin bincike kan harin jirgin sama da ya kashe mutane da dama a ƙauyen Tudun Birni dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

A wata sanarwa ranar Litinin ya ce gwamnati ta kudirin aniyar ganin cewa hari makamancin wannan bai sake faruwa ba ana gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa an jefa bam ne kan mutanen ƙauyen lokacin da suke gudanar da taron Maulidi.

Tun da farko rundunar sojan Najeriya ta amsa alhakin kai harin inda ta ce an kai shi ne a bisa kuskure.

Gwamnan ya ce tuni ya tura jami’an gwamnati ya zuwa Æ™auyen domin zaÆ™ulowa tare da ceto waÉ—anda abun ya shafa.

“Na kuma bayar da umarnin É—auke waÉ—anda suka jikkata ya zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko domin samun kulawar gaggawa. Gwamnati ta dauki nauyin kuÉ—in maganinsu dana É—awainiyarsu.” a cewar sanarwar.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...